Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 24:22 - Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Za ku kasance da doka iri ɗaya wa baƙo da kuma wa haifaffen ɗan ƙasa. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

22 Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 24:22
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”


“ ‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’ ”


Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.


Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.


“ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.


Sai Musa ya yi wa Isra’ilawa magana, suka kuwa kai mai saɓon waje da sansani, suka jajjefi shi da duwatsu. Isra’ilawa suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.


Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ