A wannan rana za ku yi taro mai tsarki, ba kuwa za ku yi aiki na kullum ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama.
A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai.
“ ‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.