ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ”
“Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,