Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 21:23 - Sabon Rai Don Kowa 2020

23 duk da haka saboda lahaninsa, ba zai yi kusa da labule, ko yă yi kusa da bagade don kada yă ƙazantar da wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji wanda yake mai da su masu tsarki.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

23 Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 21:23
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An keɓe shi domina, kada yă ƙazantar da kansa, kada kuwa yă ɓata Tentin Sujada ta wurin shiga gidan da gawa take, ko ta mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa ce. Ni ne Ubangiji.


“ ‘Ta haka za ka tsarkake Isra’ilawa daga rashin tsarkinsu, domin kada su mutu saboda rashin tsarkinsu ta wurin ƙazantar da wurin zamana wanda yake tsakiyarsu.’ ”


Wawaye makafi! Wanne ya fi girma, zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar?


Zai iya cin abinci mafi tsarki na Allahnsa, haka ma abinci mai tsarki;


Sai Musa ya faɗa wannan wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa.


“Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.


“ ‘Ku tsarkake kanku, ku kuma zama da tsarki, gama Ni ne Ubangiji Allahnku.


Dole su kasance masu tsarki ga Allahnsu, kada kuma su ɓata sunan Allahnsu. Domin sukan miƙa hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta, abincin Allahnsu, saboda haka sai su kasance da tsarki.


ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ”


Ka tuna da su, ya Allahna, domin sun ƙazantar da aikin firist da kuma alkawarin aikin firist da na Lawiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ