“Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.”
Waɗannan su ne ƙa’idodi game da cutar fatar jiki na rigar ulu, ko rigar lilin, tariyar zare, ko kayan da aka saƙa, ko kuwa duk wani abin da aka yi da fata, don furta su tsarkakakke, ko kuwa marar tsarki.
“ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,