Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 11:39 - Sabon Rai Don Kowa 2020

39 “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

39 Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 11:39
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Wanda duk yake a fili, ya kuma taɓa gawa wanda aka kashe da takobi, ko wanda ya mutu mutuwar Allah, ko ƙashin mutum, ko kabari, zai ƙazantu har bakwai.


“Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.


“ ‘Duk wanda ya taɓa jikin mai ɗiga, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma.


Duk wanda ya taɓa gadonsa dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuwa ƙazantu har yamma.


Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.


Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.


Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.


“ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana.


Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.


“ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,


Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.


“Duk wanda ya shiga gidan yayinda aka rufe shi zai ƙazantu har yamma.


Firist ɗin zai miƙa su, ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa. Ta haka zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mai ɗigar.


“Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.


“ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.


duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.


Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.


Sai na ce, “Ba haka ba ne, Ubangiji Mai Iko Duka! Ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Daga ƙuruciyata har zuwa yanzu ban taɓa cin wani abin da aka samu ya mutu ko abin da namun jeji suka kashe ba. Ba nama marar tsabtan da ya taɓa shiga bakina.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ