Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.
Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.
A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.
Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi.
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”