Farawa 8:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’