Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.
Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.
Ku kyakkece zuciyarku ba rigunanku ba. Ku juyo ga Ubangiji Allahnku, gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, yakan kuma janye daga aika da bala’i.
Ka faɗa musu, ‘Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba na jin daɗin mutuwar mugu, amma a maimako haka ya fi su juye daga hanyoyinsu su rayu. Ku juye! Ku juye daga mugayen hanyoyinku! Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila?’
“Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!”
Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus.
Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.
Kash, da a ce zukatansu za su zama masu tsorona, su kuma kiyaye dukan dokokina kullum mana, saboda kome yă zama da lafiya gare su, da kuma ’ya’yansu har abada!
Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
“Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.
Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”