10 Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
10 Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.
Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.