Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
Sai suka ce wa juna, “Tabbatacce ana hukunta mu ne saboda ɗan’uwanmu. Mun ga yadda ya yi wahala sa’ad da ya roƙe mu saboda ransa, amma ba mu saurare shi ba, shi ya sa wannan wahala ta zo mana.”