A wannan rana za su ce, “Tabbatacce wannan shi ne Allah; mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu. Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi; bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!