Farawa 41:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.
Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.