Farawa 40:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!