Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.
kada ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wata ƙasa daga cikinsu ba, ba ma wadda za tă iya isa ku sa ƙafarku a kai. Na ba wa Isuwa ƙasar tudu ta Seyir, ta zama tasa.
Wahayin Obadiya. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce a kan Edom. Mun ji saƙo daga wurin Ubangiji cewa, An aiki jakada zuwa ga al’ummai yă faɗa musu cewa, “Ku tashi, mu tafi mu yi yaƙi da ita.”