Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.
Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa ’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu.