Saboda motsi mai zurfi da zuciyarsa ta yi da ganin ɗan’uwansa, sai Yusuf ya gaggauta ya fita, ya nemi wuri yă yi kuka. Ya shiga ɗakinsa ya yi kuka a can.
Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan ’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.
Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.