Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”
“Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.
Sa’ad da ya kai wani wuri, sai ya dakata domin yă kwana, gama rana ta riga ta fāɗi. Ya ɗauki dutse daga cikin duwatsun wurin, ya sa shi ya zama matashin kansa, sa’an nan ya kwanta don yă yi barci.
“Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji.
Sai Iliya ya ce wa Elisha, “Ka dakata a nan; Ubangiji ya aike ni Betel.” Amma Elisha ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai kuma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka suka gangara zuwa Betel.