In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.
Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.