Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.
Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi.
“Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.