Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa.
Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.
“Na hallaka waɗansunku kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra. Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.
Saboda haka, muddin ina raye,” in ji Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, “tabbatacce Mowab za tă zama kamar Sodom, Ammonawa kuma kamar Gomorra, ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri, ƙasa marar amfani har abada. Raguwar mutanena za su washe su; waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu.”
“Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.
Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.
shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.
Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)
Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!”
An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta.
Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato, ’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su.
A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”