Yayinda harshen wuta ya yi sama daga bagaden, sai mala’ikan Ubangiji ya haura cikin harshen wutar. Da ganin wannan Manowa da matarsa suka fāɗi da fuskokinsu har ƙasa.
Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace.