Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 10:32 - Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

32 Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al'ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 10:32
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne ’ya’yan Nuhu maza uku, daga gare su ne kuma duniya za tă cika da mutane.


Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.


Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.


Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.


Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.


Amma ku, ku yi ta haihuwa, ku ƙaru; ku yaɗu a duniya, ku yi yawa a bisanta.”


Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya.


Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.


To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.


(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)


(waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar).


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ