Ezra 9:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 dokokin da ka bayar ta wurin annabawa lokacin da ka ce, ‘Ƙasar da za ku mallaka, ƙasa ce marar tsarki, mutanenta sun ɓata ta da ƙazamin hali, ƙazamin halinsu ya ɓata ko’ina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Umarnan da ka umarta ta bakin bayinka annabawa cewa, ‘Ƙasar da kuke shiga don ku mallake ta, ta ƙazantu da ƙazantar al'umman da take cikinta. Ƙazantarsu ta cika dukan ƙasar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.