Ezra 8:36 - Sabon Rai Don Kowa 202036 Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki36 Suka faɗa wa wakilan sarki da masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis umarnan sarki. Su kuwa suka taimaki mutane, da kuma Haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.