Ezra 8:34 - Sabon Rai Don Kowa 202034 Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki34 Aka ƙidaya dukan kome aka kuma auna, sa'an nan aka rubuta yawan nauyin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.