Ezra 6:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 Sai Isra’ilawa waɗanda suka dawo daga bauta suka ci tare da duk waɗanda suka keɓe kansu daga halin ƙazanta na Al’ummai maƙwabtansu, don su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki21 Mutanen Isra'ila waɗanda suka komo daga zaman talala suka ci tare da kowane mutumin da ya haɗa kai da su, ya kuma keɓe kansa daga ƙazantar al'umman ƙasar, domin ya bi Ubangiji Allah na Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.