Sarki ya aika da wannan amsa. Zuwa ga Rehum shugaban sojoji, Shimshai marubuci da kuma sauran abokansu waɗanda suke zama a Samariya da kuma sauran wurare a Kewayen Kogin Yuferites. Gaisuwa.
Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus.
Ya kamata sarki yă sani cewa mun je yankin Yahuda, zuwa gidan Allah mai girma. Muka ga mutanen suna ginin haikalin da manyan duwatsu, suna sa katakai a bangon. Ana aikin da ƙwazo, aikin kuma yana cin gaba sosai, suna kuma lura da shi.