Ezra 5:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.