Ezra 5:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 “Saboda haka Sheshbazzar ya so ya aza harsashin gina gidan Allah a Urushalima. Tun daga wancan lokaci har zuwa yau ana kan gina shi amma ba a gama ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Sheshbazzar kuwa ya zo ya aza harsashin ginin Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Tun daga wannan lokaci, har yanzu ana ta gininsa, har yanzu kuma ba a gama ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.