Ezra 4:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 sai suka zo wurin Zerubbabel da kuma wurin shugabannin iyalai, suka ce, “Bari mu taimake ku ginin domin mu ma muna addu’a ga Allahnku yadda kuke yi, muna miƙa masa hadaya tun lokacin Esar-Haddon sarkin Assuriya wanda ya kawo mu nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 sai suka tafi wurin Zarubabel, da shugabannin gidajen kakanni, suka ce musu, “Ku yarda mana mu yi ginin tare, gama muna yi wa Allahnku sujada kamar yadda kuke yi, muna kuma ta miƙa masa sadaka tun kwanakin Esar-haddon, Sarkin Assuriya, wanda ya kawo mu nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.