Ezra 3:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Sai Yeshuwa da 'ya'yansa da danginsa, da Kadmiyel da 'ya'yansa, da 'ya'yan Hodawiya, da 'ya'yan Henadad, duk Lawiyawa ne, suka yi shugabancin aikin ginin Haikalin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.