Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezra 2:63 - Sabon Rai Don Kowa 2020

63 Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

63 Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezra 2:63
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.


Zai tsaya a gaban Eleyazar firist, wanda zai nemi masa shawara ta wurin Urim a gaban Ubangiji. Da umarninsa, da shi da dukan jama’ar Isra’ilawa za su fita, da umarninsa kuma za su shiga.”


Sauran hadaya ta garin za tă zama ta Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayun da aka yi ga Ubangiji ta wuta.


Sauran hadaya ta garin zai zama na Haruna da ’ya’yansa; sashe mafi tsarki ne na hadayar da aka yi ga Ubangiji ta wuta.


Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.


“ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.


Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya


Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.


Ya nemi nufin Ubangiji amma bai sami amsa daga wurin Ubangiji ko ta wurin mafarki, ko ta wurin Urim, ko ta wurin annabawa ba.


Game da Lawi ya ce, “Tummim da Urim na mutumin da ka nuna masa tagomashi ne. Ka gwada shi a Massa; ka yi faɗa da shi a ruwan Meriba.


Ta wurin miƙa masa sashi mafi kyau, ba za ku zama masu laifi a wannan batu ba; ta haka ba za ku ƙazantar da tsarkakakkun hadayu na Isra’ilawa ba, ba kuwa za ku mutu ba.’ ”


Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”


Ya sa masa ƙyallen maƙalawa a ƙirji, ya kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirjin.


“ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari.


Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki.


Ba za a toya shi da yisti ba; na ba su yă zama rabonsu daga cikin hadayun da ake ƙonawa da wuta, abu ne mafi tsarki, kamar hadaya don zunubi da laifi.


Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,


Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ