Yeshuwa da ’ya’yansa maza, da ’yan’uwansa, da Kadmiyel da ’ya’yan Yahuda (’yan zuriyar Hodawiya), da ’ya’yan Henadad, da ’ya’yansu da ’yan’uwansu, dukansu Lawiyawa ne, suka haɗa kai cikin duban masu aikin gidan Allah.
A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.