Ezra 10:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam, ya yi wa Ezra magana, ya ce, “Mun yi wa Allahnmu rashin aminci, gama mun auri mata baƙi daga mutanen ƙasar, amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.