Ezra 10:18 - Sabon Rai Don Kowa 202018 A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki18 Ma'aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.
A wata na biyu na shekara ta biyu, bayan sun komo gidan Allah a Urushalima, sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, Yoshuwa ɗan Yozadak da sauran ’yan’uwansa (Firistoci da Lawiyawa da duk waɗanda suka komo Urushalima daga bauta) suka fara aiki, aka zaɓi Lawiyawa daga masu shekaru ashirin da haihuwa zuwa waɗanda suka wuce haka don su dubi aikin ginin gidan Ubangiji.