Ezra 10:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.