Ezra 1:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Sai sarki Sairus ya fitar da kayan da suke na haikalin Ubangiji waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya sa a haikalin allahnsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin Haikalin Ubangiji, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya ajiye su a haikalin gumakansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.