Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre.