A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko.
A hannunsa na dama ƙuri’a don Urushalima za tă fito, inda zai kafa dundurusai, ya ba da umarni kisa, a yi kururuwar yaƙi, a kafa dundurusai a kan ƙofofi, a gina mahaurai a kuma yi ƙawanya.
Dawakansa za su yi yawa har su rufe ke da ƙura. Katanga za su girgiza saboda motsin dawakan yaƙi, kekunan doki da keken yaƙin sa’ad da suka shiga birnin da aka rushe katangar.