Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ezekiyel 17:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

3 Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ezekiyel 17:3
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ka sa kakaki a leɓunanka! Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji domin mutane sun tā da alkawarina suka kuma tayar wa dokata.


Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa, tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.


Ya sarki kai ne itacen nan! Ka yi girma da ƙarfi; girmanka kuma ta kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko’ina a duniya.


“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa.


Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.


“Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar.


Masu fafarar mu sun fi gaggafa mai firiya a sararin sama sauri; sun fafare mu a kan duwatsu suna fakon mu a jeji.


Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji.


Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji.


Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!


Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba,


Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.


ta karya kan tohonsa da yake can bisansa ta kai ƙasar ciniki, inda ta shuka shi a birnin ’yan kasuwa.


Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi; ya yi tsayi ainun kansa ya kai cikin gizagizai.


Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ