Esta 8:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.