Esta 8:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Lambun yana da fararen labulen da aka rataye da shunayya na lallausan lilin, da aka ɗaura da igiyoyin fararen lilin, da yadin jan garura, haɗe da zoban azurfa a kan ginshiƙin farin ƙasa. A nan, akwai kujeru na zinariya da na azurfa a kan daɓe mai ado da aka yi da duwatsu masu daraja, da farin ƙasa, da fararen duwatsun wuya, da waɗansu duwatsu masu tsada.