Esta 5:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, “Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa'an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa'an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna.” Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |