Aka yi makoki sosai da azumi, da kuka mai zafi a cikin Yahudawa a kowane lardin da aka kai doka da kuma umarnin sarki. Mutane da yawa suka kwanta a cikin tsummokin makoki da kuma toka.
Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”
Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma ’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.”
Sai Esta ta kira Hatak, ɗaya daga cikin bābānnin sarkin da aka ba shi aikin lura da ita, ta umarce shi yă yi tambaya me ke damun Mordekai da kuma me ya jawo haka.