Esta 4:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Aka yi makoki sosai da azumi, da kuka mai zafi a cikin Yahudawa a kowane lardin da aka kai doka da kuma umarnin sarki. Mutane da yawa suka kwanta a cikin tsummokin makoki da kuma toka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa da rigunan makoki a cikin toka suka kwanta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.