Esta 4:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 “Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 “Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |