Gama in kin yi shiru a wannan lokaci, taimako da ceto zai zo daga wani wuri saboda Yahudawa, amma ke da gidanki za ku hallaka. Wa ya san ko saboda irin wannan lokaci ne kika sami wannan muƙami?”
“Ka tafi, ka tattara dukan Yahudawan da suke Shusha, ku yi azumi saboda ni. Kada ku ci ko ku sha, dare da rana har kwana uku. Ni kuwa da bayina za mu yi azumi yadda kuke yi. Idan aka yi haka, zan tafi wurin sarki, ko da yake wannan karya doka ce. Idan na hallaka, to, na hallaka.”