Esta 3:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Sarki ya ce wa Haman, “Ka riƙe kuɗin, ka kuma yi da mutanen yadda ka ga dama.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Sa'an nan ya ce masa, “Da kuɗin, da mutanen duk an ba ka, ka yi yadda ka ga dama da su.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.