Esta 2:23 - Sabon Rai Don Kowa 202023 Sa’ad da aka bincika labarin aka kuma iske gaskiya ne, sai aka rataye hafsoshin nan biyu a wurin rataye mai laifi. Aka rubuta dukan wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki23 Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.